Kwas ɗin Turanci da ma'aikatanka za su kai har ƙarshe.
Tutoro yana ba kowane ma’aikaci nasa malamin Turanci na AI. Darussan suna da inganci kamar na malamin da ke koyar da mutum ɗaya, kuma suna sa ma’aikata su riƙa ɗokin dawowa kullum.
Fara
Zaɓi lokacin ganin yadda yake aiki
Farawa daga $9 ga kowane ma’aikaci a wata. Ka soke biyan kuɗi duk lokacin da ka so.
Yadda Tutoro ke aiki · minti 2
Duba yadda yake aiki
Rufe bidiyon
An kai sabon mataki
A1 → A2
+ 138 XP
Yau ka fi kowace rana samun maki
Nasara a karawar mutum da mutum
Zagaye 3 da 1
Ka gama ayyukan yau
3 / 3
Streak na kwanaki 30
Kowace rana, ba fashi
+ tsabar kuɗi 250
Kyautar mako
Sabon mataki
A2 → B1
Matsayi na farko a liga
Na 1 cikin 30
Ka samu sabon malami
Katie
Duka daidai
Amsoshi 12 cikin 12 daidai
An kammala sashe
Tafiye-tafiye
Cikakkiyar jimla ta farko
Ka faɗa da babbar murya
Darussa biyar a jere
A zama ɗaya
Ka samu sabuwar shiga
Ka kashe 5 000
Sabon mataki
B1 → B2
Ka ci gwajin magana
A gwaji na biyu
Kamfanoni sun amince da mu
500
+
kamfanoni
suna horar da ma'aikatansu da Tutoro
1M
+
ma'aikata
suna koyo kullum
87
%
masu amfani a kai a kai
har yanzu suna koyo bayan kwanaki 90
Northbeam
ALTAVIA
Quadra
helioworks
Verado
Abin da kamfaninka zai amfana da Tutoro
Mintuna 15 kawai a rana a waya, ba sai an tsara lokacin shiga aji ba. Ga amfanin hakan ga kamfaninka.
Turancin da ke kawo ciniki
49% na shugabanni sun ce rashin fahimtar juna ya rusa wata yarjejeniyar kasuwanci da ƙasashen waje. Tutoro yana inganta Turancin ma'aikatanka, a farashin da zai iya kaiwa kashi ɗaya cikin 50 na kuɗin malami na musamman.
Horon da ma'aikatanka ba za su tsallake ba
AI ya taimaka wajen inganta iya magana da Turanci fiye da malamai. Tutoro yana sa ma’aikata su saba koyon Turanci kullum, kuma wasannin koyo suna sa 88% na ma’aikata su fi jin daɗin karatu.
Haɓaka ƙwarewar ma'aikatanka, rage kuɗin ɗaukar sababbi
Kamfanonin da suke ƙarfafa koyo suna riƙe ma'aikata da ƙarin 57%, kuma sauya matsayi a cikin kamfani yana ƙaruwa da 23%. Hakan yana rage maka buƙatar ɗaukar sababbin ma'aikata daga waje.
Kwatanci da wasu hanyoyi
Me ya sa Tutoro ya fi?
Ma'aikatanka su yi koyo yadda ya musu. Kai kuma ka rage aikin gudanarwa, ka san kuɗin da za ka kashe tun da wuri.
Farashi ya danganta da tsarin biyan kuɗi da yawan ma'aikata
Darussan rukuni
Malami na musamman
Tutoro
Kuɗin kowane ma'aikaci
$180 zuwa $320 a wata
$40 zuwa $120 a awa
Daga $9 a wata
Jadawalin karatu
Darussa a ƙayyadaddun lokuta
Sai ka yi ajiyar lokacin darasi tun da wuri
Ka yi koyo duk lokacin da ka samu dama, ko da minti 15 ne kawai
Koyo bisa buƙatar kowa da ƙarfafa gwiwa
Kowa yana koyo da sauri iri ɗaya, abubuwan wasa kuma kaɗan ne
Daidaita darasi da buƙatunka ya danganta da malami
Darussa sun dace da matakin kowane ma’aikaci da burinsa, wasannin koyo kuma suna sa ya ci gaba da sha’awar koyo
Bibiyar ci gaba ga sashen ma'aikata
Rahotannin halartar darussa
Sashen kula da ma'aikata bai cika ganin ci gaba ba
Allon bayanai da ke sabuntawa nan take + rahotannin ci gaba
Faɗaɗa koyo ga duk ma’aikata
Ƙarin rukunai da wahalar tsara su
Kowane sabon ma'aikaci, ƙarin kuɗi da ƙarin aikin gudanarwa
Ka haɗa duk ma'aikatanka a koyon cikin sauƙi
Yadda za ka fara
Yadda yake aiki
Ka sayi guraben koyo da kanka, ka gayyaci ma’aikatanka, kowa ya fara koyo tun da yammacin ranar.
Zaɓi yawan mahalarta
Ka zaɓi yawan ma’aikata da tsawon lokacin da za ka biya.
Gayyaci ma’aikatanka
Ka liƙa jerin adiresoshin imel ko ka tura wa kowa mahaɗin shiga guda ɗaya.
Suna fara magana da Turanci
Da zarar sun danna mahaɗin, sai su fara darasinsu na farko.
Bibiyi ci gabansu
Ka ga Streak, darussan mako da ci gaban matakin kowa a allo ɗaya.
Ci gaba da koyo
Dalilin da ya sa ba sa daina koyo
Darasi na gaske: ka yi magana da bakinka
Ka yi magana. Malaminka yana amsawa, yana bayani, yana ba ka atisaye yayin da kuke tattaunawa.
Yi atisayen kowace irin tattaunawa
Gwada hirar neman aiki, tattaunawa da likita ko shiga labarin kasada. Ko ka ƙirƙiri naka yanayin.
Zaɓi wanda za ka tattauna da shi
Kowane malami da salon furucinsa da halayensa. Zaɓi wanda ka fi jin daɗin tattaunawa da shi.
Gano abin da za ka gyara
Bayan kowane darasi, duba makinka da kurakuran da kake yawan maimaitawa.
Kalmomin da ba za ka manta ba
Kalmomin da ka kusa mantawa za su riƙa dawowa cikin ƙananan wasanni har ka riƙe su sosai.
Koyo mataki-mataki, ba gungurawa ba
Kowane darasi yana kai ka gaba a taswirar. Ka kammala wata duniya, sai ta gaba ta buɗe maka.
Ɗaga matakinka. Da gaske!
Ƙirƙiri ɗan wasanka. Kowane darasi yana ƙara masa mataki, yana kuma taimaka masa ya hau lig ta gaba.
DON SASHEN MA'AIKATA
Za ka san ko ma’aikatanka suna koyo, ba sai ka tambaya ba
Ka ga waɗanda suke koyo, ci gabansu da matakin Turancin kowa a allo ɗaya. Ba sai ka bi ma’aikata ɗaya bayan ɗaya kana tambayar inda suka kwana ba.
Yadda ma'aikata ke amfani da manhajar
Kwanaki 30 da suka gabata · bayanan misali
Guraben da ake amfani da su
Ka ga yawan guraben da ka biya da ma’aikata suke amfani da su kowane mako
Matakin Turancin kowane ma'aikaci
Muna sabunta matakin kowane ma'aikaci (A1 zuwa C1 bisa ma'aunin CEFR) yayin da yake koyo.
Ayyukan kowane ma’aikaci
Mintunan koyo a mako, darussa da Streak
Rahotanni a shirye duk lokacin da sashen kuɗi ya buƙata
Sauke bayanan da kake gani a allo a matsayin fayil ɗin CSV.
Su wa Tutoro ya fi dacewa da su?
Ga waɗanda ƙarin iya Turanci zai sauƙaƙa musu aikin kowace rana.
Fara
Masu taimaka wa abokan ciniki
Sayarwa
Injiniyanci
Otal-otal da gidajen abinci
Cinikin dillali
Kiwon lafiya
Tallace-tallace
Labarun nasara
Abin da ya canza a kamfanoni uku
A da, muna shan wahala wajen sa ma'aikata su ci gaba da koyon Turanci. Da Tutoro, suna jin daɗin koyo kuma ba sa fasa karatu. Suna ganin damar amfani da shi a matsayin wata alfarma mai amfani daga kamfanin. Yanzu ma'aikatanmu sun fi jin daɗin aikinsu.
Shugaban sashen kula da ma’aikata
Northbeam
Yanzu ma'aikatanmu sun fi ƙarfin gwiwa wajen taimaka wa kwastomomi daga ƙasashen waje. Sun fi iya fahimtar juna, kuma ba sa yawan tura matsaloli ga shugabanni. Suna magance abubuwa da kansu, kwastomominmu kuma suna samun kulawa mafi kyau.
Shugaban sashen taimakon abokan ciniki
Altavia
Yanzu muna ganin amfanin kuɗin da muke kashewa wajen horar da ma'aikata sosai. Rahotannin Tutoro suna nuna mana waɗanda suke koyo, ci gaban da suke samu da inda suke buƙatar ƙarin horo. Muna yanke shawara bisa bayanai na gaske.
Babban jami'in gudanar da ayyuka
Helioworks
Farashi
Daga $9 ga kowane ma'aikaci a wata
Ma'aikata nawa za su yi koyo?
Ka ba duk ma'aikatanka damar ci gaba da koyo a farashi ɗaya mai rangwame.
ga kowane ma'aikaci a wata
Darussan rukuni za su ci
Darussan keɓaɓɓu da malami za su ci
Mu lissafa kuɗin tare
Idan masu koyo sun haura 1,000, za mu tsara farashi na musamman ga kamfaninka, da rangwamen yawan mutane da takardar biyan kuɗi. Ma'aikatanmu na tallace-tallace za su yi lissafin tare da kai.
Tanadi lokacin ganin yadda yake aiki
Tsawon rajista
masu koyo
Tsarinka na Tutoro
Soke duk lokacin da ka ga dama
Ma'aikata nawa za su koya?
Ka sa ma’aikatanka su ci gaba da koyo cikin jin daɗi, duk a farashi ɗaya mai rangwame.
Tambayoyin da aka fi yi
Ta yaya za mu fara amfani da Tutoro a kamfaninmu?
Ka buɗe asusun kamfaninka, ka zaɓi yawan ma'aikata sannan ka gayyace su. Kowa zai samu darussan Turanci da suka dace da matakinsa da burinsa. Kana son ganin yadda Tutoro yake aiki tukuna? Ka zaɓi lokacin da za mu nuna maka.
Nawa ne kuɗin Tutoro, kuma yaya ake biya?
Kuɗin Tutoro yana farawa daga $9 ga kowane ma'aikaci a wata, kuma za ka fara da aƙalla ma'aikata 5. Ka biya da kati ko ka samar da takardar biyan kuɗi kai tsaye a shafin kamfaninka.
Zan iya miƙa gurbin koyo na wani ma’aikaci ga wani?
I, idan ma'aikaci ya bar aiki ko ya daina buƙatar amfani da Tutoro, ka ba wani gurbin nasa. Ba sai ka sayi sabon gurbi duk lokacin da wani ya maye gurbinsa ba.
Zan iya ƙara ko rage guraben karatu a duk lokacin da nake so?
Ka ƙara ko ka rage gurabe gwargwadon buƙatarka, amma su kasance aƙalla 5. Yadda kuɗin zai canza ya danganta da sharuɗɗan biyan kuɗin da ka zaɓa.
Me ma'aikata za su koya da Tutoro?
Tutoro ya haɗa duk abin da ma'aikatanka suke buƙata don koyon Turanci a manhaja ɗaya. Akwai darussa da malamin AI, atisayen magana, sauraro da karatu, da tambayoyin da za su amsa. Yana duba yadda suke furta kalmomi, ya nuna musu abin da suka yi daidai da abin da za su gyara nan take.
Shin Tutoro yana daidaita darussa da matakin Turancin kowane ma'aikaci?
I. Tutoro yana tsara wa kowane ma'aikaci darussan da suka dace da matakinsa da burinsa. Atisayen da ke kama da wasa suna sa koyo ya daɗe yana ba shi sha'awa.
Ma'aikata suna buƙatar lokaci nawa don koyo a kowace rana?
Ko minti 15 sun isa ma'aikaci ya yi karatu, duk lokacin da ya samu dama. Babu ƙayyadadden lokacin aji, kuma ba sai ya yi rajistar halartar darasi tun da wuri ba.
Ta yaya Tutoro ke ƙarfafa ma'aikata su ci gaba da koyo?
Tutoro yana haɗa darussan da suka dace da kowane ma’aikaci, wasannin koyo, lada da atisayen da ke buƙatar ma’aikata su shiga a dama. Hakan yana ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da koyo har ya zama al’adar kowace rana.
Shin sashen kula da ma'aikata zai iya bibiyar ci gaban kowane ma'aikaci?
Eh. A allon kula da asusun kamfaninka, za ka ga yadda kowane ma’aikaci yake koyo da ci gaban da yake samu. Sashen kula da ma’aikata zai iya ganin waɗanda suke yin darussa da yadda kowa yake ƙara ƙwarewa.
Shin ma'aikata suna buƙatar adireshin imel na kamfani?
A'a. Lambar gayyata ba ta da alaƙa da adireshin imel. Duk wanda ya yi amfani da ita ne zai samu gurbin. Idan ma'aikaci ya riga ya na amfani da Tutoro da asusunsa na kansa, zai ci gaba da Streak ɗinsa, ligarsa da kalmomin da ya tara. Gurbin kawai zai shiga asusun da yake da shi.
Aƙalla ma'aikata nawa ake buƙata?
Ma’aikata 5 kawai sun isa ka fara amfani da Tutoro a kamfaninka. Ya dace da ƙananan kamfanoni da waɗanda suke bunƙasa.
Ka saba koyo, ka ga ci gaba
Ka ba ma’aikatanka hanya mafi sauƙi ta koyon Turanci. Darussa masu daɗi da suka dace da buƙatar kowa, kuma suna samun lokacin yin su cikin kowace ranar aiki.
Fara
Tanadi lokacin ganin yadda yake aiki